BINCiken GASKIYA:APC na Adamawa da Wakili Boya Sun Yaudari Jama’a Game da Rawar da Suka Taka a Aikin Titin Jabilamba
Sashen jihar Adamawa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kwanan nan ya danganta Rt. Hon. Aliyu Wakili Boya da taimakawa wajen ganin an fara aikin gyaran babban titin Jabbi-Lamba–Malabu–Belel, wanda ke karkashin gwamnatin tarayya kuma kimarsa ta haura naira biliyan 26. A cikin wasu sanarwar da suka yadu sosai, jam’iyyar ta gabatar da Hon. Boya a matsayin jagoran da ya sa aka amince da aikin daga bangaren gwamnatin tarayya.
Sai dai, binciken gaskiya da wannan jarida ta gudanar ya nuna cewa ko da yake Hon. Boya ya nuna sha’awa da goyon baya ga aikin titin, kuma yana iya yiwuwa ya nemi a sanya aikin cikin manyan abubuwan da gwamnati ke baiwa fifiko, da’awar cewa shi ne kadai ya samar da aikin ba gaskiya ba ce, domin akwai wasu mahimman abubuwa da aka kau da kai daga gare su.
Bayanan hukuma sun nuna cewa a watan Mayun 2025, Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC) ta amince da kashe naira biliyan 26.829 domin gyaran titin Jabbi-Lamba–Malabu–Belel, inda aka bai wa kamfanin China Yuan Skypond Ltd kwangilar aikin. Sai dai kuma, takardun kasafin kudi daga gwamnatin tarayya sun bayyana cewa aikin an fara gabatar da shi ne tun shekarar 2018, kuma an saka wani bangare na kudaden a cikin wasu kasafin kudi tun kafin Hon. Boya ya fara wannan zangon nasa a Majalisar Wakilai.
Rahotanni da dama, ciki har da na Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, sun tabbatar cewa duk da cewa aikin yana samun kudade daga kasafin kudi a wasu shekaru da suka gabata, aiwatar da aikin na fuskantar jinkiri sosai. A tsakiyar shekarar 2025, manyan sassa na titin ba a taba su ba har yanzu, kuma kwangiloli ba su fara aiki yadda ya kamata ba.
Masu sharhi suna ganin cewa ikirarin APC wata hanya ce ta neman karbuwa a idon jama’a. Ayyuka masu girma irin wannan na bukatar shiri na tsawon lokaci, hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma bincike na fasaha—wannan ya fi karfin dan majalisa guda daya. Ko da Hon. Boya ya nuna goyon baya ga aikin a Majalisar Tarayya, babu wata shaida ta gaskiya da ke nuna cewa shi ne ya kawo kwangilar ko kuma ya aiwatar da aikin kai tsaye.
Haka kuma, binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa wani allon aiki da ke wurin ya nuna suna kamfanin Decency Associates Limited (RC: 491766), wanda aka yi rijista da Hukumar Rijistar Kamfanoni (CAC) tun a shekarar 2003. Amma bayanan daga CAC sun nuna cewa ayyukan da aka rijista da wannan kamfani su ne shigo da kaya da fitar da su (import and export of general goods) ba aikin gine-gine ba, wanda hakan ke haifar da tambayoyi kan cancantar kamfanin wajen gudanar da irin wannan babban aiki.
Kammalawa:
Ikirarin APC na Adamawa cewa Hon. Wakili Boya ne ya samar da aikin titin Jabilamba abin karantsaye ne. Labarin ya kau da kai daga tarihin aikin na dogon lokaci kuma ya yi wa rawar da dan majalisar ya taka karin haske fiye da yadda ta ke. Don haka, wannan ikirari na da ruɗani kuma ya kamata a yi hattara wajen yarda da shi.