Shugaban Karamar Hukumar Jada, Salihu, Ya Yabi Fintiri Kan Lambar Yabon NUT Da Tech Public
Shugaban Karamar Hukumar Jada, Hon. Salihu Mohammed, ya yaba wa Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, bisa samun manyan lambobin yabo guda biyu na kasa — wato lambar yabo daga Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) a matsayin Gwamna Mafi Kyawu wajen Ayyukan Ilimi, da kuma Tech Public Service Innovation Award saboda kirkire-kirkire a bangaren fasaha da gwamnati.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Jada ranar Lahadi, Salihu ya bayyana lambobin yabo din a matsayin “lambobin yabo masu kyau kuma da suka dace,” yana mai cewa sun nuna irin kokari da bajintar Gwamna Fintiri a fannin ilimi, ci gaban fasaha, da tafiyar da mulki nagari.
Ya ce lambar yabo ta NUT ta tabbatar da jajircewar Gwamna Fintiri wajen farfado da harkar ilimi a jihar ta hanyar gyaran makarantu, daukar malamai kwararru, da aiwatar da manufofi da suka inganta sakamakon karatu.
“Gwamna Fintiri kullum yana sanya ilimi a gaba a cikin shirin gwamnatinsa. Tsarin karatun kyauta, gyaran makarantu fiye da 500 a fadin jihar, da biyan albashin malamai akan lokaci sun dawo da kwarin gwiwa a ilimin gwamnati,” in ji Salihu. “Wannan yabo daga Kungiyar Malamai ya nuna gaskiya da sadaukarwa da gwamnan ke nunawa.”
Salihu ya kuma yaba wa gwamnan bisa samun lambar yabo ta Tech Public Service Innovation, yana mai cewa hakan na nuni da yadda Jihar Adamawa ke zama cibiyar kirkire-kirkire ta fasaha da ingantaccen tsarin mulki.
“Ta hanyar kirkirar sauye-sauye na fasaha a harkokin gwamnati, kula da bayanai, da sa ido kan ayyukan gwamnati, gwamnatin Fintiri ta kawo gaskiya da inganci cikin gudanar da mulki,” in ji shi. “Wannan lambar yabo hujja ce cewa Adamawa yanzu tana samun girmamawa a matakin kasa wajen kirkire-kirkire.”
Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa nasarorin gwamnan sun zama abin koyi ga sauran kananan hukumomi wajen aiwatar da manufofin da ke fifita ilimi, ci gaban matasa, da amfani da fasaha.
“Salon jagorancin Gwamna Fintiri ya saukaka mana a matakin kananan hukumomi mu bi sahunsa wajen kawo cigaba,” in ji Salihu. “Muna alfahari da abin da ya cimma, kuma muna da tabbacin cewa ci gaba da mayar da hankali kan raya dan Adam zai kai Jihar Adamawa mataki mafi girma.”
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Fintiri, yana mai jaddada cewa hadin kai da fahimtar juna su ne mabuɗin ci gaba mai dorewa.