Adamawa 2027: Girei ya yi alkawarin kawo gyare gyare a fannin ilimi, lafiya da samar da ayyukan yi.

Dr Salihu Bakari Girei, wanda ke neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Adamawa, ya kaddamar da wani shirin ci gaba mai matakai 10, wanda ya bayyana a matsayin cikakken tsarin aiki da zai hanzarta ci gaba, rage talauci tare da sake fasalin tattalin arzikin jihar.

Girei, tsohon ma’aikacin gwamnati da ya yi aiki a matakin jiha da na tarayya, ya ce hangen nesansa ya ginu ne kan shekaru na gogewa a harkokin mulki da aiwatar da manufofi a fannoni daban daban. Yana da digiri hudu na jami’a, ciki har da digirin digirgir, kuma ya yi aiki sosai a fannin ilimi, shugabanci da ci gaban cibiyoyi.

Ya ce duk da irin arzikin noma da ma’adinai da Adamawa ke da shi, jihar na ci gaba da fuskantar koma baya a fannin bunkasa jarin dan Adam, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi. A cewarsa, matsalar tsaro da rikice rikicen kabilanci sun kara tsananta talauci tare da rage saurin ci gaban tattalin arziki.

Dan takarar na APC ya ce shirinsa na da nufin kawo saukin gaggawa a fannoni kamar samar da abinci, kiwon lafiya, tsaro da ayyukan yi, tare da aza tubalin ci gaba mai dorewa ta hanyar koyar da kwarewa, sarrafa amfanin gona da gyaran hukumomi.

Shirin ya kunshi fannoni goma da suka hada da ilimi, noma, bunkasa ma’adinai, raya yankunan karkara, kiwon lafiya, wasanni, tsaro, karfafa matasa, hukumomin gargajiya da gyaran aikin gwamnati.

A bangaren ilimi, Girei ya yi alkawarin gyara makarantu, inganta kwarewar malamai da magance matsalar yaran da ke waje da makaranta. Ya ce kwarewar da ya samu a hukumar SUBEB za ta taimaka wajen zuba jari a gine gine, horar da malamai da bayar da tallafi musamman ga masu aiki a karkara.

A fannin noma, ya bayyana shirin fadada amfani da injina, inganta samun kayan aiki da bunkasa masana’antar sarrafa amfanin gona domin kara darajar kayayyaki da samar da ayyukan yi. Ya kuma ce za a karfafa tsarin ban ruwa da kungiyoyin manoma.

A fannin kiwon lafiya, Girei ya ce gwamnatinsa za ta gyara asibitoci, karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na farko tare da bayar da kulawa kyauta ga masu rauni a al’umma. Ya kuma yi alkawarin kafa asibitin koyarwa da karfafa jawo kwararrun likitoci.

Ya bayyana karfafa matasa a matsayin ginshikin shirinsa, inda ya mayar da hankali kan koyar da kwarewa, kasuwanci da fasahar zamani domin magance rashin aikin yi.

Haka kuma ya yi bayani kan inganta ababen more rayuwa a karkara, karfafa tsaro ta hanyar hadin kan al’umma da kuma bai wa hukumomin gargajiya muhimmiyar rawa a shugabanci.

A fannin aikin gwamnati, ya yi alkawarin biyan albashi a kan lokaci, karin girma bisa cancanta da sauye sauyen fasaha domin inganta aiki, tare da kula da walwalar masu ritaya.

Ya ce za a fara aiwatar da shirin cikin kwanaki 100 na farko idan aka ba shi dama, sannan a ci gaba da gyare gyare har zuwa 2031.

Girei ya ce zai shugabanci gwamnati cikin gaskiya, rikon amana da hadin kai, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa kyakkyawan shugabanci zai iya sauya yanayin tattalin arzikin Adamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *